Ciwon Sukari Nau'in Farko

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ciwon Sukari Nau’in Farko


Allurar Insulin Hoto: Medical News Today


Gabatarwa

Ciwon sukari nau’in farko, shi ne a Turance ake kira type 1 diabetes. Ciwo ne da yake faruwa sakamakon ƙaranci ko rashin samuwar sinadarin insulin a jiki. Kenan, da zarar sashen jiki mai suna fankiris ya gaza samar da sinadarin insulin ko kuma ya rage yawan samar da sinadarin har ta kai ga bai wadaci jini ba, abin da zai biyo baya shi ne yawaitar sinadarin bilkodi; sukarin jini a cikin jini wadda wannan kuma shi ne ciwon sukari nau’in farko (Type 1 diabetes).

Sababi

Masana harkar lafiya da masu ruwa da tsaki cikin harkar ciwon sukari da suka haɗa da Hukumar Lafiya ta Duniya, (2021); Watson, (2020); Cleveland Clinic, (2021) da sauran su, sun haɗu a kan cewa ruɗani da garkuwar jiki ke samu wajen yin aiki ita ke kaiwa ga illata fankiris har ta kai ga ta kasa samar da sinadarin insulin. Ko me ke haddasa wannan ruɗewa ta ƙwayoyin garkuwar jikin ɗan’adam, sun ce ba a kai ga gano hakan ba. Saboda haka sai suka sallama cewa wannan Min Indillahi ne; wato abin da suka kira natural a Turance.

Wannan nau’in cuta ya fi kama ƙananan yara, dalilin da ya saka ake riƙa kiranta da juvenile ko kuma childhood-onset a lokutan da suka shuɗe kamar yadda ya zo a Hukumar Lafiya ta Duniya (2021).

Alamomi

  • Yawan yin fitsari.
  • Yawan jin ƙishin ruwa.
  • Dawamma a cikin jin yunwa.
  • Rashin nauyi.
  • Gajiya (Ba tare da an yi aiki ba).

Su ne alamomin da suka fi bayyana a tare da mai ɗauke da wannan nau’in ciwon sukari, Hukumar Lafaiya ta Duniya (2021).

Magani

Allurar Insulin ita ce kaɗai maganin da aka iya ganowa tare da cewa mai ɗauke da wannan nau’in ciwon sukari dole a yi masa ita kullum. Sai dai, masu ɗauke da wannan nau’in ciwon sukari yawansu bai haura kashi goma cikin ɗari ba (10%).

Manazarta:


Cleveland Clinic (2021). Diabetes: An Overview. 9500 Euclid Avenue, Cleveland, Ohio 44195 | 800.223.2273

Hukumar Lafiya ta Duniya (2021). Diabetes. An Ciro a shekarar 2021 data shaken: https://www.who.int/news-room/fact-sheet

Hukumar Lafiya ta Duniya (2021). The Global Diabetes Compact, What You Need to Know. An ciro a shekarar 2021 daga shafin: https://cdn.who.int/media/docs/defaultsource/diabetes/gdc_need_to_know_web.pdf

Watson S. (2020). Everything You Need to Know About Diabetes. An Ciro a shearer 2021 data shafin: https://www.healthline.com/health/diabetes


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub